Jami’an sojin Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda Tara, tare da ceto wasu mutane biyu dauke da kudin fansa a yankunan Gagiram da Magumeri a jihar Borno.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanal Kanal Uba Sani ya fitar a ranar Asabar, ta ce an kashe ‘yan ta’addan a wasu hare-hare daban-daban.
Sani ya ce baya ga kwato makamai, da yawa daga cikin maharan sun kuma samu munanan raunuka, inda suka tsere.

Sanarwar ta ce jami’an sun ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, inda sojojin na Operation HADIN KAI suka gudanar da sintiri cikin nasara a yaki da ta’addanci bayan samun sahihin bayanan sirri kan ‘yan ta’addan Boko-Haram a kusa da Goni Dunari a karamar hukumar Magumeri ta jihar Borno a ranar 10 ga Oktoba 2025.

Ya ce bayan samun bayanan, jami’an suka yi musayar wuta da ƴan ta’addan, inda aka kashe ‘yan ta’addan biyar, yayin da sauran 19 suka tsere.
Daga cikin abubuwan da aka kwato sun hada da bindiga daya ta AK-47, mujallu biyar, wayar hannu daya, wuka da dai sauransu.
A wani samame daban-daban, kuma kakakin ya ce sojojin da ke kan babura sun yi musyar wuta da mayakan Boko Haram akan hanyar Gajiram zuwa Bolori mai nisan Mile 40 Gajiganna kusa da kauyen Zundur a jihar.
Ya ce a yayin musayar wutar, an kashe ‘yan ta’adda hudu, yayin da wasu kuma suka gudu zuwa cikin daji.
Sannan sojojin sun ceto Mista Modu Kinnami mai shekaru 55, da Mista Bukar mai shekaru 57, dukkansu daga Guzamala, tare da buhu mai dauke da Naira dubu 750,000.
Binciken farko ya nuna cewa mayakan Boko Haram sun bukaci a biya su kudin fansa Naira Miliyan biyu, da kuma sabbin wayoyin hannu guda biyu domin kafin sakin dan uwan wanda suka kama.
A cewarsa jimlar kuɗaɗen sun kai naira miliyan huɗu da ɗari uku da hamsin da Biyar.