Jami’an rundunar sojin Najeriya na Operation FANSAN YAMMA sun samu nasarar kubtar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara.

Babban kwamandan runduna ta biyu, kuma kwamandan sashi na uku na Operation FANSAN YAMA, Manjo Janar Chinedu Nnebeife ne jagoranci jami’an da suka kai ga samun nasarar.

Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar soji ta biyu, Laftanar Kanal Polycarp Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Okoye ya ce a wata ziyarar aiki da suka kai ofishin ‘yan sintiri na Babanla a ranar Alhamis, ta jagoranci sojoji zuwa dajin Babasango, inda suka ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su.

Ya kara da cewa ziyarar ta biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a kusa da Idofin a karamar hukumar Omu-Aran, inda aka kashe wasu ‘yan kasuwa uku a kauyen Olegbede.

Oba Oluwole ya danganta hare-haren da yadda mazauna yankin ke kusa da dajin Babasango.

Kwamnadan ya ce za su ci gaba da gudanar da ayyukan da suke yi na kawar da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka a dajin.

Wasu ‘yan bindiga ne dai dauke da makamai suka kai hari kauyen Oke-Ode a karamar hukumar Ifelodun ta jihar, inda suka kashe ‘yan banga da mafarauta akalla 15 a karshen watan Satumba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: