Majalisar dattawa ta ba da wa’adin makonni biyu ga bangaren zartarwa da su gabatar da cikakken rahoton ci gaban da aka samu kan aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024, da kuma hasashen kasafin kudin shekarar 2025, kafin yin duba da tsarin kashe kudade na matsakaicin lokaci MTEF.

Shugaban kwamitin majalisar mai kula da harkokin kudi, Sanata Sani Musa ne ya bayyana hakan a lokacin wata ganawa da tawagar tattalin arzikin shugaban kasa Bola Tinubu, karkashin jagorancin ministan kudi da kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun, a zauren majalisar.
Sanata Musa ya bayyana cewa majalisa na buƙatar cikakkun bayanai game da ayyukan, don tantancewa yadda ya kamata da kuma hasashen da ke cikin takardar MTEF.

Acewarsa ba za su ci gaba da MTEF ba tare da fahimtar yadda kasafin kudin 2024 ya gudana zuwa yanzu ba.

Sanata Sani Musa ya ce sun ba su zuwa ranar 23 ga Oktoba don dawowa da kuma bayar da rahoton da aka tattara kafin su kalli MTEF na shekarar 2026 mai kamawa.