Majalisar dokokin jihar Benue ta amince da bukatar da gwamnan Jihar Hyacinth Alia ya gabatar mata na neman rancen Naira biliyan 100 don gudanar da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin jihar.

Majalisar ta amince da rokon gwamnan ne a wani zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Juma’a.

A cikin wata wasika da shugaban majalisar ya karanta a gaban zauren Majalisar, ya ce gwamna Alia zai yi amfani da bashin ne wajen gudanar da ayyuka da suka hada da gyare-gyare, samar da kayan aiki ga manyan asibitoci 23, gyara da gina makarantun kimiyya, kammala ayyukan tituna da gadoji da ake gudanarwa, gina cibiyoyin koyon sana’o’i, da kafa makarantu masu inganci a dukkanin mazabun tarayya.

Har ila yau rancen zai dauki nauyin ginawa da kuma samar da kayan aiki na Jami’ar Aikin Gona, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Binue, da dai sauransu.

Bayan gabatar da bukatar gwamnan majalisar ta amince da bukatar da baki daya, inda ta bukaci gwamnan da ya yi amfani da kudaden cikin adalci domin ci gaban jihar.

Sai dai kuma jam’iyyar PDP a jihar ta yi watsi da amincewar, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin tunani da rashin kula da yanayin tattalin arzikin da al’umma ke fuskanta.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na jihar Tim Nyor, ya fitar ya ce babu gaskiya da rikon amana a cikin ciyo bashin, yana mai gargadin cewa matakin na iya jefa Jihar Benue cikin yanayin bashin mara dorewa.

Jam’iyyar ta bukaci Majalisar da ta dakatar da matakin da ta dauka na amincewa, tare da yin aiki da gaskiya ta hanyar bincike.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: