Rundunar sojin Najeriya ta ce sojoji hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da biyar suka samu raunuka a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai musu hari a sansaninsu da ke Ngamdu a karamar hukumar Kaga akan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Da yake tabbatar da harin a cikin wata sanarwa mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai Laftanal Kanal Uba Sani, ya ce ‘yan ta’addan da dama sun rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce jami’an na Operation HADIN KAI sun yi nasarar dakile harin ta’addancin da aka kai a yankin Ngamdu, bayan yin musayar wuta cikin gaggawa da jami’an sojin kasa hadin gwiwa da na sama suka yi.

Acewarsa ƴan ta’addar sun yi amfani da manyan makamai, da ababan fashewa inda suka kai’wa sojojin hari a sansaninsu, sai dai ya ce jami’an su ma sun yi amfani da karfinsu tare da mayar da martani wanda hakan ya kai ga samun nasara akan ƴan ta’addan.

A jiya juma’a ne dai Rahotanni daga jihar Borno na bayyana cewa jami’an soji da dama ne su ka mutu bayan wani hari da mayakan Boko Haram su ka kai musu a sansaninsu da ke Ngamdu da ke ƙaramar hukumar Kaga a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: