Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ASUU ta umurci dukkan rassanta da ke fadin Najeriya da su fara yajin aikin gargadi na mako biyu daga gobe Litinin.

Shugaban kungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da suka gudana a yau Lahadi a hedkwatar kungiyar da ke Jami’ar Abuja.
Shugaban ya ce matakin fara yajin aikin gargadi ya zama wajibi, bayan gwamnati ta gaza yin abin da ya dace dangane da bukatunta, duk da sanarwarwa kwanaki 14 da suka bayar a ranar 28 ga Satumba, amma biyan bukatun ya ci tura, ba tare da wani cikakken martani daga hukumomin da abin ya shafa ba.

Shugaban na ASUU ya kuma umarci dukkan ƴaƴan kungiyar na Ƙasa da su dakatar da ayyukansu da misalin 12:00 na dare yau, tare da fara yajin aikin wayewar garin gobe Litinin.

Sai dai gwamnatin tarayya ta yi gargadi ga kungiyar malaman jami’o’i ta Ƙasa ASUU, tare da yin barazanar babu aiki, babu albashi, matukar suka fara yajin aiki a yau Litinin.