Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kaddamar da bincike kan wasu matafiya biyu da aka same su da kudaden kasashen waje, dala miliyan 6.1 da kuma fam miliyan 53,000 a filin sauka da tashin jirgen sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.

EFCC ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Ta ce Jami’an hukumar na shiyyar Ikoyi ne suka kama wadanda ake zargin Mamud Nasidi da Yahaya Nasidi.

EFCC ta ce jami’an hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ne suka kama wadanda ake zargin a lokacin da ake gudanar da bincike da ta saba yi.

EFCC ta kara da cewa mutanen biyu da suka iso Najeriya daga birin Adis Ababa na Ƙasar Dubai, inda suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja, inda suka kasa bayyana kudaden da suka kai dala miliyan 6,180 da fam miliyan 53,415 a hannunsu, kamar yadda doka ta tanada.

Hukumar EFCC ta kuma ce ta kwace wayoyin hannu uku na wadanda ake zargin a lokacin da aka kama su.

Bayan kama su da farko an mika su ga ma’aikatar harkokin wajen kasar kafin daga bisani a mika su ga hukumar EFCC domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: