Gwamnan Jihar Benue Hyacinth Alia ya yi kira da a hada kai don zurfafa dimokuradiyya da gina makoma mai kyau a jihar.

Gwamna Alia ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron da jam’iyyar APC ta shirya wanda aka gudanar a karshen makon nan a garin Makurdi.
Gwamnan ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyar bisa jajircewarsu da manufofin gwamnatin sa.

Taron ya kuma shaida ficewar wasu shugabannin siyasa da magoya bayansu daga jam’iyyar PDP, ADC, da Labour Party zuwa APC.

Gwamna Alia ya bayyana sauya shekar a matsayin wata alama ta amincewa da ayyukan gwamnatinsa. da gagarumin goyon baya daga manyan masu ruwa da tsaki a fadin jam’iyyar ya nuna cewa kokarinsu na samar da sakamako mai kyau.
Ya kuma yi karin haske kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu, inda ya ce rashin tsaro a fadin kananan hukumomin Jihar ya ragu sakamakon kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya.
Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na bunkasa noma, inda ya sanar da sabbin kudade don tallafawa bangaren manoma.
Gwamnan ya kuma gargadi ‘yan kwangilar da ake zargin sun damfari jihar wajen samar da taki, inda ya sha alwashin cewa za a tuhume su.
A bangaren ilimi kuwa, Alia ya ce ana ci gaba da gyare-gyare sosai a makarantun firamare domin inganta yanayin koyo da koyarwa. sannan ya bai’wa ma’aikatan gwamnati tabbacin ci gaba da biyan albashi cikin gaggawa.