Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda rayuwar matasan Najeriya ke kara tabarbarewa dangane da halin da ake ciki a kasar.

A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a ranar Lahadin nan, ya bayyana cewa ya gana da gungun matasa daga sassan jihohin Arewa 19, wadanda suka bayyana takaicin su kan zaben da aka yi na magudi da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
Ya ce matasa sun damu da kada kuri’unsu da ba a kirga ba kuma rashin shugabanci da tsare-tsare na yin illa ga rayuwar su da sana’o’insu.

Acewarsa koda a jiya sai da ya sake karbar wata tawagar matasa daga jihohin Arewa 19 karkashin jagorancin Alhaji Adamu Bappa Gombe, inda ya ce sun damu matuka game da yadda kuri’unsu ba sa yin tasiri, da kuma yadda rashin kaykkyawan shugabancin da manufofi ke haifar da naƙasu ga rayuwarsu da kasuwancinsu.

Ya ce bayan zuwa da koken nasu ya karfafa musu gwiwa, ya kuma jaddada cewa sai ta hanyar akwatin zabe za a iya samar da canji.