Jami’an sojin Operation FANSAN YAMMA, sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a dajin Babanla da ke jihar Kwara, a daidai lokacin da jami’an ke kara kaimi wajen daƙile ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar jihar.

Acewar wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labaran rundunar soji ta 22 da ke Ilorin, Captain Stephen Nwankwo ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su ne a wani aiki na hadin gwiwa da aka gudanar a ranar Asabar, biyo bayan sahihan bayanan da suka samu kan masu garkuwa da mutane a yankin.

Ya ce a sumamen da sojojin suka kai kan maboyar ƴan bindingan da ke dajin na Babanla, suka yi nasarar ceto Oluwabusayo Taiwo mai shekaru 25, da danta mai shekaru uku Taiwo Irayomide, wadanda aka yi garkuwa da su a Oke-Ode a ranar 28 ga Satumban da ta gabata.

Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu wadanda aka ceto na samun kulawar gaggawa a Asibiti, daga bisani kuma a sadasu da ‘yan uwansu.

A wani samame na daban kuma a wannan rana, sojojin da ke gudanar da sintiri a kan hanya sun ceto Mista Mohammed Sanni mai shekaru 40 mai sana’ar sayar da shayi a yankin Garkarima. Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun tsere ne bayan da suka hangi tawagar jami’an da ke sintiri, inda suka bar wanda suka kaman.

Kakakin rundunar ya kara da cewa, sun gano wasu bindigogi guda biyu a wurin da lamarin ya faru, ya ce wanda abin ya shafa na samun kulawa shima a asibitin.

Kwamandan rundunar ya yabawa sojojin bisa jajircewa da daukar mataki cikin gaggawa, yana mai ba da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kawo ƙarshen ‘yan ta’adda a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: