Hukumar kula da zirga-zirgar sufurin jiragen Ƙasa ta Najeriya NRC ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata hanyoyin jiragen Ƙasa da suka hadar da Abuja Legas Kaduna da kuma Warri.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Callistus Unyimadu ta fitar a ranar Asabar, ta ce hakan babbar barazana ce da kawo cikas ga ayyukan jiragen Ƙasa a lokacin da ya ke tsaka da tafiya.
Sanarwar ta ce Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke kula da layin dogo da ke Abuja zuwa Kaduna ne suka kama wadanda ake zargin, Ibrahim Abdullahi mai shekaru 22 dan Hayi Rigasa, da Sani Ibrahim mai shekaru 24 na Layi Turaki Rigasa.

An kama su ne a Kaduna bisa laifin lalata hanyan layin dogon da aka yi a unguwar tashar jirgin kasa ta Rigasa.
Kamen na su ya biyo bayan ganowar ne a ranar Juma’a da misalin karfe 12:30 na rana, cewa an yanke wata waya, tare da cire ta daga daya daga cikin na’urorin hukumar da aka sanya a cikin ginin.

Mutanen da ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu, inda suka ce sun sayar da wayar da suka sace ga wani Musa, a kan kudi Naira 90,000, inda kowanne wanda ake tuhuma ya karbi naira 30,000 a matsayin kasonsa, yayin da wani dan kungiyarsu, Abdulwahab Yakubu na Rigasa, ke amsa sauran laifukan.
Sannan jami’an na kokarin kama sauran wadanda ake zargin tare da kwato kayan da suka sace.