Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba za’a kawo karshen radadin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi a wani sabon mataki na bunkasar tattalin arziki.

Shettima ya bayyana hakan ne a yayin taron samar da makamashi da sabuntawa ta Najeriya (NREIF) a ranar Talata a Abuja, Shettima ya ce zuciyar shugaba Bola Ahmed na tare da ‘yan Najeriya kuma a halin yanzu suna jin radadin da suke ciki.
Taron wanda Hukumar raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA) ta shirya ta shirya ne domin neman saka hannun jari wajen samar da kayayyakin da ake sabunta su a cikin gida.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa taron goron gayyata ne, na kafa Najeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi sabuwa a Afirka, kuma canjin makamashin Najeriya ya ba da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410 tsakanin wannan lokaci zuwa shekarar 2060.

Ya ce daga cikin wannan ana bukatar sama da Naira biliyan 23, don fadada hanyoyin samar da makamashi da kuma hada miliyoyin ‘yan Najeriya da har yanzu suke rayuwa cikin rashin makamashi, amma bayan samun dama, babban burinsu shi ne samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin gigawatts 277 na jimlar da aka samar nan da shekarar 2060.
Yayin da bukatar fiye da zuba jari, yana bukatar kirkire-kirkire, da sadaukarwa.
Taken taron na bana Shi ne, Aiwatar da Manufofin Najeriya na farko, gudanar da ci gaban al’amuran Cikin Gida da Samar da Makamashi, ba kawai akan lokaci ba ne, amma yana da matukar muhimmanci.
Yunkurin shi ne dabarun masana’antu na Najeriya, inda yayin da su kara dagewa kan makomar hanyoyin samar da makamashi na Afirka a nan gida.
Ya kara da cewa, a karkashin tsarin, an tattara sama da dala miliyan 400 na sabbin alkawurran sa ka hannun jari a cikin darajar samar da makamashin da ake sabuntawa a Najeriya.
A nasa bangaren, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce Najeriya a shirye take ta jagoranci sauye-sauyen makamashin da ake samu a Afirka.
A bangaren samar da wutar lantarki, manufar farko ta Najeriya ta nuna aniyar tabbatar da cewa zamani na fasahar samar da makamashi mai tsafta, tun daga kan na’urori masu amfani da hasken rana har zuwa batir, da sauran kayan amfani a fadin kasar.