Wasu da a ke zargi mayakan Boko Haram ne sun halaka sojoji a ƙauyen Kashimiri da ke ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno.

An kashe sojojin biyar a wani hari kwanton ɓauna da yan Boko Haram su ka kai musu

Bayan soji biyar da a ka kashe akwai ƴan ƙungiyar tsaron haɗin gwiwa uku da a ka kashe.

Sai kuma wasu da dama da su ka jikkata ciki har da kwamandan sojin runduna ta 222 da ke Konguda, yayin da wani soja guda ya bace.
Jami’an sojin da ke aikin kakkaɓe ƴan Boko Haram sun haɗu da ajalin nasu ne yayin da su ke komawa zuwa Bama.
Wani da ya tsallake harin ya shaida cewar an kai su ne don shafe ƴan Boko Haram bayan samun bayanai a kan wata haduwa da su ke shirin yi daga sassa daban-daban.
Ya ce sun samu nasarar tarwatsa sansaninsu sannan sun kubutar da mata da ƙananan yara sai kuma a ka kai musu hari yayi da su ke hanyar komawa.
A cewarsa, kwamandansu ya mutu da kuma wasu soji biyar sai jami’an haɗin gwiwa uku da a ka kashe
Ya ce sojin sun yi amfani da babura ne saboda wahalar shiga wajen
Sai dai daga bisani an kai ƙarin jami’an tsaro da su ka kai musu ɗauki a wajen.