Gwamnan Jihar Bala Mohammed ya rattaba hannu kan dokar nada masarautu 13 da hakimai sama da 111 a fadin jihar.

Har ila yau ya kuma sanya hannu kan dokar,soke masarautar Sayawa da kuma kafa masarautar a karamar hukumar Tafawa Balewa.
Hakazalika gwamnan ya rattaba hannu kan shirin bayar da gudunmawar fansho na kananan hukumomi, inda ya yi alkawarin wanke badagurbin kudaden fansho da kuma kudaden da ake bin ma’aikatan kananan hukumomin da suka yi ritaya.

Bugu da kari, an rattaba hannu kan dokar Karin Kammala Kasafin Kudi na shekarar 2025 don tallafawa gudanar da ayyukan raya kasa da tsare-tsare da gwamnatinsa ta bullo da su cikin sauki.

Sabbin masarautun sun hada da Burra, Duguri, Dambam, Bununu, Lere , Darazo, Jama’a, Lame, Toro, Ari, Warji , Giade, Gamawa, da kuma Sayawa Zaar.
A jawabin a yayin sanya hannun a gidan gwamnatin Jihar a ranar Talata, gwamnan ya yi gargadin a kan sanya siyasa ko tauye aiwatar da sabbin dokokin da aka kafa, inda ya umurci hukumomin tsaro da su dauki matakin da ya dace akai.
Gwamna ya kuma umarci kwamishinan shari’a da sakataren gwamnatin jihar da su gaggauta buga jaridu da kwafin dokokin da rarraba ga dukkan hukumomi da cibiyoyin da abin ya shafa don aiwatar da su.