Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya kaddamar da asibitin koyarwa na Jami’ar Arewa maso yamma wato North-West University, wanda tsohon gwamna kuma Sanata Aliyu Wamakko ya kafa, inda ya bayyana shi a matsayin wani babban ci gaba da al’ummar jihar za su dunga tunawa da su har abada.

Mai magana da yawun gwamnan Abubakar Bawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce a yayin jawabin gwamna Aliyu a wajen bikin kaddamar da asibitin,ya ce samar da asibitin wani babban mataki ne na bunkasa ilimin likitanci da kiwon lafiya a Sokoto da yankin Arewa maso yamma.

Acewarsa asibitin zai zama cibiyar kwararrun kula da lafiya, ilimin likitanci, da kuma bincike na zamani.

Gwamnan ya bukaci ma’aikatan asibitin da su yi aiki da dukkan kwarewarsu, mutunci, da tausayi wajen yiwa al’umma hidimi.

Aliyu ya kuma bayyana kokarin da gwamnatin sa ke yi na karfafa fannin kiwon lafiya a jihar, inda ya bayyana wasu nasarorin da aka samu da suka hada da daukar likitoci ‘yan asalin jihar 122 aiki kai tsaye, da tura ma’aikatan malaman jinya da ungozoma 1,675 a wuraren kiwon lafiya, tare da kafa dokar tilasta wa kwararrun likitoci a yankunan karkara aiki na tsawon shekaru biyu.

Anasa bangaren Sanata Aliyu Wamakko, wanda ya samar da jami’ar, ya ce asibitin na wakiltar sabon aiki a fannin kiwon lafiya, ilimin likitanci, da bincike a Sokoto, harma da arewa maso yamma, da Najeriya baki daya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: