Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekaru 17 mai suna Auwal Dahiru da wasu mutane biyar da ake zargin su da cire idon ‘yar uwarsa mai suna Rukayya Muhammad mai shekaru bakwai a wani yunkurin neman kudi a kauyen Bayan Dutse da ke Wailo a unguwar Kubi a karamar hukumar Ganjuwa ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar Ahmed Wakil ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Wakil ya ce lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Oktoban nan, bayan samun rahoto daga wani Muhammad Adamu na Kauyen Bayan Dutse a ofishin ‘yan sanda na Soro.

Adamu ya yi zargin cewa da misalin karfe 8 na dare Auwal ya yaudari kanwarsa zuwa cikin wani daji da ke kusa da wurin, inda anan ne ya cire mata idon.

Kakakin ya ce bayan samu rahoton Baturen ‘yan sanda na yankin Aliyu Goni, ya yi gaggawar jagorantar tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargin, inda kuma nan take aka garzaya da wanda aka hallaka zuwa Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin kula da lafiyarsa, inda kuma likitoci su ka bayyana cewa ba za ta sake gani ba.

Wakil ya kuma bayyana cewa an kama wasu da ake zargi da aikata laifin da suka hada da Mohammed Rabiu mai shekaru 19 da Saleh Ibrahim mai shekaru 20 da Nasiru Muhammad na garin Soro da Hassan Garba na garin Soro da Garba Dahiru mai shekaru 43.

Ya kara da cewa binciken farko ya nuna cewa mutane za su yi amfani da idanun yarinyar ne domin neman yin kudi, inda wadanda ake zargin suka amsa laifinsu.

Wakil ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: