Kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce gwamna Uba Sani ya sa ke mayar da bangaren kiwon lafiya a Jihar na daban-daban a cikin shekaru biyu da yayi akan karagar mulkin Jihar.

A yayin ziyarar ban girma a gidan Sir Kashim Ibrahim Shugaban kungiyar Dr Hassan Bala Salihu, ya ce gwamnan ya samu nasarori da dama, musamman ta fuskar bunkasa kayayyakin more rayuwa da walwala da kuma horas da likitoci.
Ya ce tuni Jihar Kaduna ta amince ta biya kudaden horas da ma’aikatan lafiya na shekarar 2024 da 2025, inda ta kasance ita ce jiha ta farko a kasar nan da ta biya kudin horaswa na shekarar 2025.

Dr Salihu ya kuma ce Jihar Kaduna ce jiha ta farko a Arewacin Najeriya da ta kaddamar da dokar kula da lafiyar kwakwalwa ta zama doka tare da hada ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa a manyan asibitoci.

Haka zalika ta fara shirin hadin gwiwa tsakanin tsarin shari’a da kiwon lafiya, domin magance sanadin aikata laifuka a tsakanin matasa.
Shugaban kungiyar likitocin ya kuma yabawa jihar kan hada kan daliban likitanci, ta hanyar biyansu alawus-alawus, da kuma tsarin biyan albashin Lafiya na 2024 ga Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya.
Anashi bangaren gwamna Malam Uba Sani ya amince da bukatun kungiyar, tare da bai’wa kungiyar kyautar motar aiki don gudanar da ayyukanta.