Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Lawan Shiisu ya fitar ranar Talata a Dutse.
Ya ce jami’an rundunar sun kama wadanda ake zargin ne a ranar 18 ga watan Oktoba a Garki, Fagam da Maigatari, yayin wani samame da jami’an leken asiri suka kai a fadin jihar.

Kakakin ya ce wadanda ake zargin na cikin jerin sunayen da ‘yan sandan Jihar ke nema ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu wajen rabon haramtattun kayayyaki a jihar.

Lawan ya ce rundunar ta kama miyagun kwayoyi guda 23,944 a yayin samamen, inda ya ce biyu daga cikin wadanda ake zargin sun fito ne daga jihar Kano da jamhuriyar Nijar.
Ya jaddada kudirin Rundunar na kawar da mutane daga dabi’ar shan miyagun kwayoyi da ke ci gaba da naƙasa rayukan matasa.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.