Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta kama wasu mutane da ake zargi da kisan kai tare da kwacan ababan hawa.

Jami’in Hulda na jama’a na rundunar ƴan sandan Jihar Shiisu Lawan Adam ne ya bayyana hakan a yau Asarabar.

Adam ya ce an kama su ne ta hanyar bin matakan tsaro a wani sumaman hadin gwiwa da rundunar ta yi.

Wadanda aka kama sun hada da Haladu dan kauyen Buju da ke karamar hukumar Dutse, da kuma Safiyanu Shu’aibu dan garin Maimakawa da ke karamar hukumar Gaya a jihar Kano da ake zarginsu da yin sojan gona tare ka kishan kai.

A dai ranar 19 ga watan Octobar 2025 wadanda ake zargin da suka hada kai da wasu mutane biyu , suka Farwa Wanda aka kashe a cikin wani daji da ke hanyar Maimakawa zuwa garin Albasu da ke jihar Kano.

Yayin da suka harbe shi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa daga bisani kuma suka tsere da motarsa.

Shiisu ya kara da cewa jami’an sashin binciken manyan laifuka na Jihar ne suka gudanar da sumaman da yayi sanadiyyar kama wadanda ake zargin, inda kuma suke ci gaba da gudanar da sintirin domin kama sauran wadanda ake zargin .

Ya kuma Kara da cewa za’a mika wadanda ake zargin zuwa shelkwatar yan sanda da ke Kano dan Kara fadada bincike , tare da mika su Kota dan girbar abinda suka shuka.

A wani sumaman kuma an kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar ababan hawa, Musbahu Sabo mai shekaru 25 da ke garin Rimgim a Jihar da kuma Asabe Yahya wanda akafi sani da Reza mai kimanin shekaru 45 mazaunin garin Dan Masara da ke Dutse.

Wadanda ake zargin an kama su da mota kirar Toyoto da ake zargi sato ta suka yi.

Ya kuma Kara da cewa da akwai wasu mutane Uku da ake zargi da hada baki da suka hadar da Arma Idris, da kuma Yusuf dukkansu mazauna yankin Dan Masara ne da ke Dutse, inda za su tafi da motar daga Hadeja zuwa Dutse domin siyan motar.

Shisu ya ce za su aike da su zuwa baban shashin bincike manyan laifika na jihar dan Kara tsaurara bincike da kuma gufanar da su a gaba kotu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: