Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya gargadi ƴan siyasa a jihar da su banbance tsakanin sukar manufofin gwamnati tare da gargadin su kaucewa siyasantar da tsaro a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a gidan Sir Kashim Ibrahim a lokacin da manyan daraktoci hukumar tsarin farin kaya ta DSS suka kai masa ziyara ban girma.
Ya yi tir da irin kiyayyar da wasu ‘yan siyasa ke yi a kafafen yada labarai da ke zubar da kimar kasar nan, da sunan adawa da manufofin gwamnati da rashin tsaro, yana mai bayyana su a matsayin ‘yan adawa masu rusa dimukradiyya.

Acewar gwamnan ‘yan siyasa sun manta cewa masu rike da mukaman gwamnati za su kammala wa’adinsu tare da barin ofis, ku Najeriya za ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa.

Kazalika Gwamnan ya bayyana cewa, duk wani dan adawa zai iya sukarsa, amma dukkan wanda yayi abinda zai haifar da rashin jituwa ko bata suna ƙasa ko kuma kawo cikas ga zaman laiya, hakan na nuni cewa mutum ya zama mai tayar da rikici a cikin al’umma.
Gwamna ya kara da cewa wasu daga cikin girɓatattun siyasa da ke cikin jam’iyyar adawa, da ke kokarin nakasa dimkradiyya da tsaro, inda ya gargade da su da kada su yi amfani da damar wajen lalata tsaro a jihar da fadin Ƙasar nan.
Gwamnan ya kuma yabawa mai bai’wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu da dukkan shugabannin hukumomin tsaro da babban daraktan ma’aikatar harkokin gwamnati Adeola Ajayi bisa kokarin da suke yi na dakile matsalolin tsaro a kasar nan.
Gwamna Sani ya kuma bukaci ƴan Najeriya da su kasance masu kishin ƙasa, tare da gargadin ƴan siyasa da su daina siyasantar da lamarin tsaro.
