Gwamnatin Jihar Kebbi ta gudanar da addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar.

Taron addu’o’in da aka gudanar a Birnin Kebbi babban birnin jihar, ya hadar da malaman addinin Musulunci da na Kirista daga kananan hukumomi 21 na jihar.
A yayin jawabin gwamnan Jihar Nasir Idris ya ce akwai bukatar ci gaba da addu’o’i domin dorewar zaman lafiya, hadin kai, da zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Acewarsa babu wata jiha a ƙasar nan da za ace tana zaman lafiya dari bisa dari a halin yanzu, inda ya bayyana cewa bai kamata a dunga siyasantar da batun tsaro a ƙasar ba.

Ya kara da cewa masu ikirarin cewa babu wata alaka mai kyau tsakanin Musulmi da Kirista a jihar, kawai na yada labarin karya ne.
Gwamnan ya yabawa malaman addini da mahalarta taron da suka taru domin gudanar da addu’o’in, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa jihar Kebbi da Najeriya addu’o’in zaman lafiya, ci gaba, da wadata.
Taron wanda ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar ta shirya, na da nufin neman taimakon Allah da shiga tsakani wajen magance kalubalen da ke addabar al’umma na ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran matsalolin rashin tsaro da ke addabar al’umma.
Daga cikin wadanda suka hallarci taron akwai ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki Sanata Atiku Bagudu, tsohon Gwamnan Jihar Sa’idu Dakingari, da kuma sakataren kungiyar APC na kasa Alhaji Sulaiman Argungu.
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar, Sheikh Abubakar Riba, da Revrend Femi Olofin, mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, na daga cikin masu gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Hakazalika an kuma gudanar da karatun kur’ani mai tsarki da addu’o’i na musamman da malamai suka yi akan hadin kan kasa, tsaro, da kuma neman kariyar Ubangiji ga ‘yan kasa.
