Rundunar sojin Najeriya karkashin jagoranci Operation whirl stroke sun kama wasu mutum uku da ake zargi da sojin gona a karamar hukumar Ohimini dake jihar Benue.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ahmad Zubairu ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, jiya juma’a a Makurdi.
A cewarsa an kama su ne a ranar Laraba 5 ga watan Nuwamba 2025 , yayin da jami’an ke sintiri a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu da ke ƙaramar hukumar Amoda Axis.

Waɗanda a ka kama sun hada da John Isaac dan shekaru 22 da Baba Emmanuel dan shekaru 17 se kuma Sunday Thomas dan shekaru 19 dukkan su mazauna yankin Otukpo , lokacin da ake bincika motar da suke ciki.

Sanarwa ta ce an kama su da wayar tafi da gidanka guda uku da kudi naira. 20,200.
Zubairu ya Kara da cewa binciki ya nuna cewa wadanda ake zargin na kan hanyarsu ta Zawa aikata laifi ne yayin da aka kamasu.
Ya kuma Kara da cewa zuwa yanxu an turasu Babban sashin bincikin dan Kara fadada binciki akansu.
Sannan ya yabawa shugaban da ya jagoranci sintirin Manjo Janar Moses Gara bisa ƙoƙarin da kuma nuna kwarewa kan aikin nasa.
Gara ya kuma umarci jami’an da su ci gaba da sanya idanu wajen tabbatar da tsaro a yankin musamman a wannan lokacin na sanyi.
Ya kuma ƙara da cewa jami’an Operation whirl stroke hakkin su ne wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Bunue , Nasarawa da kuma Taraba wajen kare rayuwa da dukiyoyinsu.
Sumaman ya biyo bayan wani hari da a ka kai ƙaramar hukumar Ohimini inda a ka kashe wasu mutum hudu.
Shugaban karamar hukumar Adole Gabriel ne ya tabbatar da hakan , inda yace an kashe wasu manona biyu a ranar Litinin yayin da aka Kara kashe wasu mutum a ranar Talata da yamma.
