Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin ya yi kira ga shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump da ya janye barazanar da ya yiwa Najeriya a baya-bayan nan, tare da bayar da hakuri a bainar jama’a kan yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da ke nauyi hakkin addini.

Ya ce kalaman Trump wadanda suka hada da gargadin yiwuwar daukar matakin sojan Amurka na kawowa ƙasar hari, kan zargin yiwa Kiristoci kisan kare dangi, ba abu ne wanda za a amince da shi ba, kuma hakan ya sabawa ka’idojin diflomasiyya da dokokin ƙasa da ƙasa.
Sanata Barau ya ce a matsayin Najeriya na kasa mai cin gashin kanta, ba za ta amince da duk wani nau’i na tsoratarwa ko tsoma baki ba kan aiwatar da harkokin ƙasarta.

Dan majalisar ya kara da cewa Najeriya ba ta ji dadin kalaman Trump ba, yana mai jaddada cewa ikon kasa da mutunta juna dole ne su jagoranci alakar kasa da kasa.

Barau ya bayyana hakan ne dai a ranar Juma’a ta cikin wani faifan bidiyo da aka fitar, inda ya bukaci Trump da ya janye kalamansa tare da fitowa ya nemi afuwar Najeriya.
