Gabanin zaben Najeriya da ke tafe a ranar asabar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa ta lalata tabar wiwi da nauyin ta ya kai kilogram 7,286. a wani gandun daji dake jihar Edo.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na hukumar ya wallafa a shafinta na Twitter, sanarwar ta bayyana cewa hukumar ta gudanar da wani sumamene a ranar laraba bayan da ta sami wani rahoton sirri na cewa wasu bata gari sun shiga dajin dauke da jakukuwa wanda ke dauke da ganyen.
Hukumar ta ce tana zargin mutanan na kokarin rar-raba ganyen ne zuwa jihohin kasar gabanin zabe mai zuwa a ranar asabar.

Hukumar ta kara da cewa jami’anta sun dauki dogon lokaci suna artabu da mutanen kafin daga bisani jami’anta suka sami nasara.

Kana sanarwar ta kara da bayyana cewa jami’anta sun kwace bindigu kirar AK47 da dai sauran makamai daga mutanen.
Hukumar ta ce tana zargin mutanan na