Mataimaki ga dan takarar shugaban kasa Kashim Shattima ya jajantawa yan kasuwar Monday markert tare da ba su kyautar naira milyan 100 bayan gobarar da kasuwar ta yi.

Kashim ya baiwa yan kasuwar Monday markert naira milyan 100 sakamakon iftilain da ya samu kasuwar na gobara da ta tashi a ranar Lahadi .

Shattima ya ce ya je jihar Borno cikin gaggawa dajin faruwar wannan lamarin domin tausayawa da yakeyiwa alummar.

Ya ci gaba cewa yana mai jajantawa gabakiya daya.

Cikin sakon kashim ya ce zuwan na sa ba shi kadai bane harda dan takarar shugaban kasa wato Bola Ahmad Tunubu Kuma zai je domin yin jaje bisa asarar da aka tafka tare shugaban kasa.

gwamnan jihar Baba Gana Umara Zulum bisa faruwar wannan gobara da ma alumma A jiya Lahadi ne dai gobara ta tashi a babbar kasuwar da ake Kira da Monday markert inda a ka yi asarar dukiya mai tarin yawa,kuma har ya zuwa yanzu ba a San mene ya haddasa gobarar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: