Biyo bayan karar da jaruma Amina Amal ta shigar take karar Jaruma Hadiza Gabon kan zargin taci zarafinta inda ta bukaci kotu da ta sanya Gabon ta biyata diyyar ma’udan kudade.

A yanzu dai rikicin ya dauki sabon salo domin kuwa kotu ta sanya ranar 10 ga watan gobe domin cigaba da saurarar kara kuma an dauki tsawon lokaci ba’a samu sammacin kotun ya isa ga ita jaruma Gabon ba.

Sai dai a yayin da Jaruma Gabon ta shirya tsaf domin tafiya aikin Umara, jami’ai sun risketa a filin sauka da tashin jiragen sama inda suka damka mata sammacin ta kuma karba hannu bibiyu.

A daya bangaren ma dai a farkon makon da muke ciki ne dai akayi sulhu tsakanin jarumi Mustapha na Buraska da kuma jaruma Hadiza Gabon din a wata kotu dake nan Kano.

Allah ya kyauta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: