Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da korar Dr. Ferdinand Giadom daga matsayin da yake kai na shugaban aikin HYPREP.

Sanarwar korar Dr. Ferdinand Giadom ta fito ne ta shafin Twitter na fadar shugaban kasa.

An kirkiro aikin HYPREP ne domin magance matsalar gurbata Neja-Delta da sinadarai masu illa.

A yayin da aka tabbatar da tsige tsohon mai rike da makamin, nan take sanarwar ta bayyana cewa an nada wani wanda zai jagoranci aikin.

Farfesa Nanibarini Zabbey ne zai maye gurbin Giadom, fadar shugaban Najeriyan ta kuma ce zai fara aiki ne ba tare da wani bata lokaci ba.

Sanarwar ta fito daga ma’aikatar muhalli ta kasa wanda ta tabbatar da cewa Giadom ya bar ofishinsa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: