Ƙungiyar likitoci masu son a Najeriya sun koma bakin aiki bayan yajin aikin gargaɗi da su ka tsunduma na kwana biyar.

Likitocin sun ƙuracewa asibitocin gwamnati sakamakon rashin cika alkawuran da aka yi musu a baya.

Sai dai sun janye yajin aikin bayan nazarin alƙawuran da gwammnati ta yi a ganawarsu ta ƙarshe.

A sanarwar da buƙatun da su ka miƙa akwai Karin albashi ga likitocin masu neman ƙwarewa da kuma ɗaukar sabbin likitoci don  maye gurbin waɗanda su ka bar aiki.

Sannan sun bukaci a janye ƙudirin hana sabbin likitocin barin Najeriya har sai sun yi shekara biyar sun a aiki a ƙasar kamar yadda aka gabatar a baya.

Shugaban ya ce gwamnatin ta yi musu alƙawarin biyansu wasu kuɗaɗe a wata na gaba.

Likitocin sun ce nan da makonni biyu masu zuwa z su duba su ga matakin da ya dace su ɗauka a kan buƙatunsu.

Gwamnatin Najeriyua na shirin yin dokar hana likitoci masu son ƙwarewa barin ƙasar har sai sun yi aiki na shekara biyar.

Sai dai likitoci da dama ne su ka bar Najeriya ganin yadda sue k kokawa a kan ƙarancin albashi da walwalarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: