Babban hafsan tsaron Najeriya Manjo Janar Christopher Musa ya yi wata ganawa da gwamnan jihar Zamfara a yau.

Gwamnan ya ganawa da babban hafsan tsaron a helkwatartar tsaro ta ƙasa da ke Abuja.

Duk da cewar babu masaniya a kan dalilin ganawar, sai dai ana zargin ganawar na da alaƙa da batun tsaro da ya shafi jihar Zamfara.

Gwamnan ya shiga helkwatar tsaron da misalin ƙarfe 12:22pm na yau, bisa rakiyar wasu mukarrabansa da kuma jami’an tsaro.

Wata majiya mai tushe ta ce an tattauna batun masu garkuwa da mutane da yan bindiga da su ka addabi jihar Zamfara.

Ganawar ta mayar da hankali a kan yadda za a kawo karshen matsalar tare da tabbatar da maganceta baki ɗaya.

Jihar Zamfara ta sha fama da hare-haren ƴan bindiga wanda hakan ya yi silar rasa rayuwar mutane da dama da kuma asarar dukiya mai yawa.

Sama da shekara goma aka shafe ana fama da matsalar yan bindiga wanda ya tilastawa da yawa barin muhallinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: