Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya a yau Litinin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Dele Alake ya sanyawa hannu a safiyar yau, ya ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin karfe 07:00PM na yamma.

Gidajen talabiji da na rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai na daga cikin wadanda za su yaɗa jawabin.

Sanarwar ta nuna yadda shugaban zai mayar da hanklai wajen yi jawaabi a kna cire tallafi mna fetur da kuma karin tsadarsa.
Haka kuma da batun shirin tafiya yajin aikin da kungiyar kwadago za ta shiga sai batun tafiya yajin aikin da kungiyar likitoci a kasar su ka tsunduma.
Idan ba a manta ba, kungiyar kwadago ta daura damarar tafiya yajin aikin gama gari a ranar Laraba bisa tsadar man fetur da tsadar rayuwa da ake fama a Najeriya.