Gwamnatin tarayyar Najeriya ta aiwatar da tsarin ba aiki ba albashi ga ƙungiyar likitocin ƙasar.

Daraktan harkokin asibiti na ma’aikatar lafiya ne ya aike da wasiƙar haka ga babban akantan Najeriya mai ɗauke da sa hannun 1 ga watan Agustan da mu ke ciki.
Kwamfin takardarv wanda kamfanin dillancin labarai ya samu ya nuna yadda gwamnatin ta ƙaddamar da tsarin ga likitocin da ke tsaka da yajin aiki.
Hakan na n uni da dakatar da biyan albashin likitocin sakamakon yajin aikin da su ka fara wanda su ka ce sun shiga bayan da gwamnatin ta gaza cika alƙawuran da ta ɗaukar musu.
Ƙungiyar ta shiga yajin aikin ne ganin yadda ta gaza biyan wasu haƙƙoƙi na kuɗi ga likitocin bayan da ta ɗauki alƙawarin biya a wani zama da aka yi a baya.

Wasiƙar da aka aikewa ofishin akantan Najeriya ta umarci ofishin da ya dakatar da albashin likitocin da su ka tsunduma yajin aikin.

Da yake mayarv da martani dangane da matakin da gwamnatin ta ɗauka, shugaban ƙungiyar Dakta Innocent Orji ya ce za su zauna a wannan ƙarshen makon tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Sannan tun fara yajin aikin da su ke ciki a yanzu gwamnatin tarayya ba ta tuntuɓesu domin yin zama da su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: