Ƙungiyar shuwagabannin kananan hukumomi a Najeriya ta taba tare da jinjinawa kotun koli bisa hukuncin da ta yanke kan basu yancin gashin kansu.

Shugaban kungiyar Aminu Muazu ne ya bayyana haka a tattaunawar da aka yi da shi a gidan talabiji na Channels.
Ya ce hukuncin da kotun ta yanke babban ci gaba ne ga kananan hukumomi.

Dangane da rike kudaden kananan hukumomi da gwamnoni ke yi, shugaban ya ce hakan y asabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Ya ce matakin zai taimaka wajen mutanen da ke kasa don ganin sun samu ci gaba a matakin karamar hukuma.
A cewar shugaban, alumma ma na cikin farin ciki dangane da hukuncin da kotun koli a Najeriya ta yanke.
A ranar Alhamis ne dai kotun ta yanke hukuncin bai wa ƙananan hukumomi dama da yancin Cin gashin kansu a Najeriya bayan da gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban kotun
Sai dai gwamnonin sun ce za su yi nazari dangane da hukuncin kotun koli.