Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga watan Yulin nan da muke ciki za a fara fuskantar ambaliyar ruwa a wasu sassan Jihohi 19 na Kasar da birnin tarayya Abuja.

Gwamnatin ta bayyana cewa ana kyautata zaton ambaliyar za ta yi barna a guraren da abin ya shafa, tare da ci gaba da yaduwar cutar kwalara a wasu Jihohin.

Ministab albarkatun ruwa da tsaftar Muhalli Farfesa Joseph Utseb ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa Ambaliyar ruwan da aka fara tun daga watan Mayun da ya gabata kadance, kuma hakan na faruwa ne sakamakon toshe magudanan ruwa.

Ministan ya ce daga watanann Manyan kogunan Kasar za su fara cika su na Ambaliya wanda hakan zai ta’azzara matsalar.

A cewarsa daga cikin Jihohin da abin zai shafa sun hada da, Jigawa, Kaduna, Nasarawa, Neja, Taraba, Kebbi, Kogi, Kwara, Ogun, Osun.

Sauran sun hada da Ondo, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Bayelsa, Delta, Edo, Benue, Anambra, da kuma Birnin tarayya Abuja.

Ministan ya kara da cewa ana hasashen ambaliyar za ta fara ne daga Kogin Kwara da na Benue.

Inda ya bukaci mazauna Jihohin da su fara shirye-shiryen kaucewa hanyoyin da abin zai shafa.

Farfesa Joseph ya ce su na ci gaba da shirye-shiryen gina wasu kananan koguna domin tara ruwan da ya yi ambaliya daga Kogin Lagdo na Kasar Kamaru, wanda Ambaliyarsa ke babbar barna a Najeriya.

Ya ce an kuma kafa wani kwamiti da zai yi aikin kare faruwar ambaliyar a daminar bana, tare da daukar kwararan matakai akan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: