Gwamnatin tarayyar Najeriya ta aike da kayan abinci jihohi 36 har da Abuja don rage radadin tsadar da ake fuskanta.

Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ne ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar yau a Abuja.
Ya ce an aike da manyan motocin tirela 20 na shinkafa ga johoji 36 har da Abuja domin ragewa mutane radadin tsadar kayan abinci da yunwa da ake fama.

A cewar ministan, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru wajen tabbatar da cewar yan Najeriya sun samu abinci.

Idan za a iya tunawa a labaran da mu ka kawo muku mun bayyana muku cewar ministan harkokin noma a Najeriya Abubakar Kyari ya ce za a karyar da farashin kayan abinci Uwa watan Janairun shekarar 2025.
Wannan dai na zuwa ne bayan da ake raderadin wasu yan Najeriya na shirin yin zanga-zanga kan halin matsi da tsadar rayuwa.