Ministan yaɗa labarai a Najeriya Mohammed Idris ya ce ƙasar Dubai ta dage takunkumin da ta kakabawa yan Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin ganawa da yan jarida yau a Abuja.

Ya ce an cimma matsaaya kuma tuni hadaddiyar daular larabawa UAE ta dage haramcin bayar da biza ga yan Najeriya.

Ya ce daga yau Litinin yan Najeriya na iya tafiyar ƙasar ta Dubai.

Duk da cewar ministan bai bayyana cikakken bayani a kan haka ba, amma ya ce kowanne lokaci daga yanzu yan Najeriya na iya tafiya kasar.

Tun a baya dai gwamnatin Najeriya ke ta cuku cuku don ganin an dage haramcin bizar ga yan ƙasar waɗanda aka haramtawa zuwa.

Hadaddiyar daular larabawa dai ta kakabawa yan Najeriya takunkumin hanasu shiga tun a watan Disaamban shekarar 2021.

Dubai ta haramtawa ƴan kasashen Najeriya da Congo shiga kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: