Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC Malam Mele Kyari ya ce a watan Agusta mai kamawa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki gadan-gadan.

Kyari ya bayyana haka ne jiya Litinin a zauren majaliar dattawa bayan da ya hakarci gayyatar da kwamitin tattalin arziki n majalisar ya yi masa.
Ya ce nan da watanni kaɗan za’a dinga fitar da ganga miliyan biyu a kowacce rana a Najeriya.

Malam Mele Kyari ya ce a halin yanzu sun dukufa don tabbatar da aikin ya kankama ganin yadda hakan zai taimakawa tattalin arziki.

Dangane da batun matatar mai ta Kaduna da Warri, Malam Mele Kyari ya ce za a fara aiki da ita zuwa watan Disamban shekarar da mu ke ciki
Ya ce an dan samu tsaiko a aikin da ake yi ta Fatakwal hakan ya sa ba ta fara aiki ba a karshen wata Maris.
Zuwa yanzu dai sun kammala shiri tsaf don fara aiki da matatar mai ta Fatalwal a watan Agusta mai kamawa