Kungiyar kwadaggo a Najeriya NLC ta yi barazanar tafiya yajin aikin wata guda a kasar bisa zargin da take yi wa majalisa na shirin rage albashin ma’aikata.

Shugaban kungiyar na ƙasa Joe Ajaero ne ya bayyana haka a taron shekara shekara da ƙungiyar ta saba yi a Legas.
Ya ce batun mafi ƙarancin albashi al’amari ne da ya shafi kasa baki daya.

Kungiyar ta ce ta na zargin majalisar dattawa da majalisar wakilai ta ƙasa na shirin cire sashe na 34 wanda zai bai wa gwamnoni damar biyan albashin da za su iya.

Ya ce ba za su lamunci hakan daga wajen gwamnoni ba a don haka su ka yi barazanar tafiya yajin aikin gama gari a kasar har na wata guda.
A ranar Alhamis dai ake sa ran shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu zai sake ganawa da kungiyoyin dangane da mafi karancin albashi
Ana sa ran kafin karshen makon gobe shugaban zai gabatarwa da majalisa sabon mafi karancin albashin ma’aikatan don mayar da shi doka.