Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake aikewa da majalisar dokoki buƙatar kara naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin shekarar 2024 da mu ke ciki.

Shugaban majalisar dokoki ta kasa Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman majalisar na yau Laraba.

Ya ce shugaban ya aike da wasikar buƙatar ƙarin naira tiriliyan 6.2 wanda za a yi wasu ayyuka da su.

A baya shugaban ya gabataar da kasafin naira tiriliyan 28.7 wanda ya sanya hannu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar da mu ke ciki.

Shugaban ya yi amfani da sashe na 58 (2) wanda ya bayar da damar yin gyara a kasafin.

Za a kashe naira tiriliyan 3.2 a a tsarin ayyuka karkashin Renewed Hope da sauran manyan ayyuka

Sai kuma tiriliyan 3 wanda za a kashe a sauran ayyukan da ake kai.

Idan majalisar ta amince za a kashe naira tiriliyan 34.9 a bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: