Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu kuma Mai tsawatarwa a majalisar Dattawa ta Sanata Ali Ndume ya yi watsi shugabancin da majalisar ta bashi na shugaban kwamitin yawon bude ido.

Ndume ya bayyana hakan ne a gidanshi da ke garin Maiduguri a yau Juma’a, inda kuma ya bayyana shi ba dan yawon bude ido ba ne.
Nadin da majalisar ta yiwa Ndume na zuwa ne sa’o’i 48 bayan tsege daga matsayin mai tsawatarwa a Majlisar.

Bayan tsege Ndume a ranar Larabar da ta gabata shugabancin jam’iyyarsa ta APC a majalisar ya maye gurbinsa da Sanata Tahir Munguno daga Borno ta Arewa.

Majalisar ta dauki matakin sauke Ndume daga kan mukamin nashi ne bayan yin wata suka akan yadda shugaba Tinubu ya ke tafiyar da salon mulkinsa a Kasar.
Bayan yin kalaman shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar ya aikewa da majalisar wasikar, inda ya bukaci da Sanata Ndume ya bayar jam’iyyar APC ya kuma koma dukkan jam’iyyar da ya yi niyya.
A dai takardar da Ganduje ya aikawa majalisar ya kuma bukaci da a sauke shi daga kujerar mai tsawatarwa a majalisar, sakamakon yin kalaman da ba su dace ba ga shugaban kasa Tinubu wanda hakan kuma ka iya kawowa gwamnatin Tinubu nakasu.
Sanatan ya ce babu wasu kalamai masu tsauri da ya yi da har majalisar za ta dauki matakin tsige shi daga mukaminsa.
Ali Ndume ya ce jam’iyyar APC ce ta bai’wa shugaban Majalisar Godswill Akpabio umarnin tsige shi daga mukaminsa.
A cewarsa shi ne ya jagoranci yakin neman zamowar shugaban majalisar ta 10 Godswill Akpabio nasarar zama shugaban majalisar ta dattawa, inda kuma bayan zabar Akpabio a matsayin shugaban Majalisar aka bashi damar zaɓar dukkan kwamitin da yake so.
Kazalika Ndume ya kara da cewa bai taba muradin zama mai tsawatarwa ba a majalisar bayan zamowarsa a matsayin jagoran majalisar dattawa ta 8.
Sanatan ya ce a dangane da batun shawarwarin da ake ba shi na ficewa daga jam’iyyar APC, ya ce shi uban jam’iyya ne domin yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar tun lokacin da shugaban jam’iyyar APC na yanzu yana mataimakin gwamnan Kano.
Ali Ndume ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin sanatoci 22 da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP domin kafa APC.