Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyatti-Allah ta MACBAN Yakubu Muhammad a Jihar Filato.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis da misalin karfe 7;40 na dare a yankin Jebu da ke karamar hukumar Bassa da ke Jihar.

Shugaban kungiyar a karamar hukumar Ya’u Idris ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shugaban ya ce kungiyar su ta na Allah-wadai da wannan mummunar aika-aikar da maharan suka aikata.

Ya ce ya zuwa yanzu sun shigar da rahotan faruwar lamarin ga jami’an ‘yan sanda a Jihar domin gudanar da bincike.

Kwamandan Rundunar Operation Save Haven Birgediya Janar M O Ago ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan marigayin, tare da bayyana cewa rundunarsu ta yi rashin jajirtaccen matashi.

Kafin hallaka Yakubu na daya daga cikin kwamitin zaman lafiya da rundunar ta kafa domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: