Mataimakin gwamnan Jihar Edo Philip Shaibu ya sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a Jihar.

Shu’aibu ya koma APC ne a yayin kaddamar da wani kwamitin gudanarwa na jam’iyyar bisa zaben gwamnan Jihar da ke tafe.

Mataimakin gwamnan na Edo ya koma APC ne bayan kotu ta mayar da shi kan mukaminsa bayan tsige shi da majalisar dokokin Jihar ta yi daga mataimakin gwamnan Jihar bisa wasu zarge-zarge da ta yi masa.

 

An kaddamar da kwamitin ne a yau Asabar, kuma ya samu halartar shugaban jam’iyyar na Kasa APC Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan Jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa da na Cross River Bassey Otu.

Sannan shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Jarett Tenebe da dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar ta APC

Monday Okpebholo da kuma Sanata Adams Oshiomole.

Philip ya koma jam’iyyar ta APC ne kwanaki biyu bayan wani hari da aka kai masa a lokacin da yake gudanar da murnar hukuncin da kotu ta yanke akansa na ci gaba da zama mataimakin gwamnan Jihar.

Harin da aka kai’wa Philip hakan ya sanya jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da shirya kai’wa Shu’aibu harin sakamakon mayar da shi mukaminsa da kotu ta yi.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: