Majalisaar dokokin Najeriya ta amince da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Majalisar dattawa ce ta amince da kudin a zaman da ta gudanar yau Talata.
A shekarar 2019 ne majalisar ta amince da naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi tare da alkawarta bibiya a kai duk bayan shekara biyar.

A amincewar da ta yi ta gamsu da bibiyar tsarin duk bayan shekara uku maimakon biyar a baya.

A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Kuma daga bisani ya mikawa majalisar bayan da ƙungiyoyin ƙwadago su ka amince a kan haka.