Wasu da ake zargi ƴan fashi da makami ne sun yi wa wasu dalibai biyu fyade a jihar Ogun.

Lamarin ya faru da ƙarfe 12:30am na daren Litinin wayewar yau Talata.
Yan fashin sun shiga jami’ar ilimi ta Tai Solarin da ke Ijagun Ijebu Ode a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar yan fashin sun fara kwace wayoyin daliban sannan su ka tafi da su zuwa wani gini da ba a kammala ba.

Rundunar yan sanda a jihar ta tabbata da faruwar lamarin.
Mai magana da yawun yan sanda a jihar Omolola Idutola ta ce sun samu labarin faruwar hakan a safiyar yau Talata kuma tuni jami’an su su ka bazama don neman waɗanda su ka yi aika aikar.
Sannan waɗanda lamarin ya faru a kansu an yi gaggawar kai su asibitin da ke jami’ar don duba lafiyarsu.