Majalisar wakilai a Najeriya ta umarci hukumar kula da wutar lantarki da ta rage karin kudin wutar da ta yi na rukunin Band A.

Umarnin na zuwa ne bayan kudirin da dan majalisa kuma shugaban kwamitin da ke lura da wutar Victor Nwokolo ya gabatar.
Majalisar ta umarci a soke karin wutar lantarkin da aka yi sannan ta bayar da umarnin bincike a kan tsadar wutar lantarkin.

Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya NERC ce ta ƙara kuɗin wanda ta ce za ta ƙara yawan adadin wutar da za a dinga samu a ƙasar har tsawon awanni 20 a kullum.

Majalisar ta ce za ta yi bincike dangane da tsadar wutar lantarkin.
Idan za ku iya tunawa dai kungiyar ƙwadago a Najeriya ta gabatar da kokenta kan tsadar wutar lantarki kuma ya na daga cikin bukatun da ta gabatarwa da gwamnatin.
Majalisar dai na ci gaba da ayyuka kain da nain tun bayan ayyana zanga-zanga da wasu matasa a Najeriya su ka ce za su yi tsakanin kwanaki goma zuwa 15 a watan Agusta.