Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta ce za ta shiga cikin zanga-zangar lumana da ake shiryawa a ƙasar.

Shugaban kungiyar na ƙasa Joe Ajaero ne ya bayyana haka yayin da yake musanta batun da ake haɗawa cewar kungiyar ta tsame hannunta daga zanga-zangar.
Ajaero ya ce hankalin ƙungiyar ya kai kan batun da ake haɗawa cewar ban da su a zanga-zangar da ake shiryawa saboda ba su su ka shirya ba.

A cewarsa labarin ba shi da tushe balle makama.

Ya ce kungiyar ta shawarci Gwamna tarayya daa ta gayyaci masu shirya zanga-zangar don tattaunawa da su a kai
Ajaero ya ce ƙungiyar ta na matukar goyon bayan zanga-zangar da ake shiryawa kan tsadar abinci da wahalhalu da ake fuskanta a ƙasar.
Haka kuma kungiyar ta sake shawartar gwamnatin da ta saurari koken jama’a a kan halin da su ke ciki don samar da mafita a kai.