Soldiers aboard a truck patrol during a violent protest by Shiite Muslims demanding the release of their detained leader Ibrahim Zakzaky on July 23, 2019 in Abuja. - At least eight people were killed in clashes between Shiite Muslim protesters and Nigerian police in Abuja on July 22, with a journalist among those shot dead in the latest bloodshed over the detention of a religious leader. A policeman was also killed in the unrest, which broke out when hundreds of protesters from the Islamic Movement in Nigeria (IMN), a Shia sect, marched demanding the release of cleric Ibrahim Zakzaky, who has been held since December 2015 on charges including terrorism. (Photo by KOLA SULAIMON / AFP)

Hedkwatar tsaro ta Kasa ta musanta wani bidiyo da ke yawo cewa ‘yan ta’adda sun kwace motocin jami’anta biyu masu sulke a Jihar Zamfara.

Sannan hedkwatar ta kuma musanta jita-jitar cewa an kashe mutane da dama wadanda ‘yan bindiga suka binne, tare kuma da jita-jitar sace mutane 150 a Jihar Sokoto.

Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

A sanarwar da Buba ya fitar kan batun kwace motocin jami’annasu a Jihar ta Zamfara, ya bayyana cewa motocin sun makale ne a cikin Tabo, a lokacin da jami’an ke kokarin korar maharan a Kauyen Kwashabawa da ke Jihar.

Buba ya ce jami’an sojojin sun kwace dukkan kayayyki masu amfani a cikin motocin domin haramtawa ‘yan bindigan yin amfani da su.

Manjo Buba ya kara da cewa bidiyon da ake yada wanda ke nuna ‘yan ta’adda na binne mutane masu yawa ba Najeriya ba ne.

Kakakin ya ce rahotan da ake yadawa kan sace mutane 150 a Jihar Sokoto, an yi hakan ne domin a dakushe nasarar da jami’an sojoji ke samu akan ‘yan ta’adda a Kasar.

Rundunar na wannan kalami ne bayan da ta hangi wani faifan bidiyo da ke nuna ‘yan ta’adda na gudanar da murnar kwace motocin jami’an sojin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: