Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana bacin ransa kan yadda aikin titin garin Garko ya ke tafiya, tare kuma da kwace aikin daga hannun dan kwangilar da aka bai’wa aikin.

Gwamnan Abba ya bayyana cewa kamfanin da aka bai’wa kwangilar aikin yaki komawa wajen aikin domin ya kammala.
Abba Kabir ya kara da cewa nan bada dadewa ba, gwamnatinsa za ta sake bayar da kwangilar aikin titin ga wani dan kwagila don kammalawa.

Sannan gwamna Abba ya shaidawa mazauna karamar hukumar ta Garko cewa zai gina masu asibiti na zamani domin inganta lafiyar al’ummar karamar Hukumar.

Kazalika gwamnan ya kuma duba yadda aikin samar da gurin aikin noman rani na Kafinchiri ya ke gudana a karamar hukumar ke tafiya.
Gwamnan ya ce aikin zai lakume Naira biliyan 2.5, inda ya ce ana san ran za a kammala bayan kammala aikin zai habaka harkokin noman rani domin inganta abinci a Jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce aikin na daga cikin kokarin gwamnatin ta Kano ta ke yi na habaka harkokin noma.