Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano KANSIEC ta bayyana cewa ta rage kudin sayan takardar tsayawa takarar shugabannin kananan hukumomin Jihar da ta sanya a Baya.

Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana hakan, a yayin taron masu ruwa da tsaki dangane da zaben kananan hukumomin Jihar.
Malumfashi ya bayyana cewa hukumar ta yi ragin ne domin yin biyayya ga umarnin kotu na saye yin duba akan kudin tsayawa takarar.

Shugaban ya ce dukkan wani dan takara da zai tsaya a matsayin shugaban Karamar hukuma zai biya naira miliyan Tara, ya yin da kuma Kansila zai biya naira miliyan hudu.

Shugaban ya ce sun yi ragin ne bayan da wasu jam’iyyar a Jihar suka shigar da su kara gaban kotu kan cewa kudin takarar da hukumar ta sanya sun yi yawa.
A baya dai hukumar ta sanyara naira miliyan 10 ga shugabannin kananan hukumomi, ya yin da kuma kansiloli za su saya fomdin akan naira miliyan 5.