Jami’an sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka fitaccen dan bindigar nan Kachalla Halilu Sububu.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Ya ce jami’an sun kashe kasurgumin dan ta’addan ne a safiyar yau Juma’a.

Halilu Sububu shi ne ubangida ga daya shararran dan bindigar nan Bello Turji da ya addabi mutanen Zamfara.

Abdul’Aziz ya ce kafin kisan dan ta’addan jami’an tsaron sai da suka yi musayar wuta da ‘yan ta’addan, a kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanki a cikin ƙananan hukumomin Moriki da Anka da ke Jihar Zamfara.

Abdul’aziz ya kara da cewa kisan dan bindigar wata babbar nasarar, ce da ta samu na kashe manyan ‘yan ta’adda a cikin shekara guda.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: