Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa NDLEA ta tabbatar da kai samame wasu daga cikin kasuwannin Maiduguri domin bincike akan abinci da magani da ake sayarwa a kasuwannin bayan ambaliyar da aka samu a garin.

Hukumar ta bayyana cewa a sumamen da kai ta kama abinci da magunguna masu yawa wadanda suka daina amfani.

NDLEA ta ce ta kai samamen ne a Kasuwar Monday Market, kasuwar Gamboru, kasuwar magani ta Gwange da dai sauransu.

Hukumar ta bayyana cewa ta kai sumamen ne bayan bayanan da ta samu kan yadda wasu ‘yan Kasuwar ke busar da magunguna da suka jike a yayin ambaliyar tare kuma da sayarwa da mutanen gari.

NDLEA ta ce hakan ne ya sanya ta kai sumamen tare da bukatar rufe kasuwanni har sai bayan ta kammala bincike domin tabbatar da ingancin kayyakkin da ake sayarwa a kasuwannin.

Hukumar ta NDLEA ta kuma tabbatar da kama abinci da magunguna da suka lalace na fiye da da Naira biliyan biyar.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da kokari wajen ganin ta tabbatar da ingancin kayayyaki a fadin Kasar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: